- Jam'iyyar PDP a jihar Osun a karkashin jagorancin Gwamna Ademola Adeleke ta rasa ɗaya daga cikin manyan kusoshinta
- Alhaji Shuaib Oyedokun ya fice daga PDP kamar yadda ya bayyana a wasiƙar da ya miƙa wa shugannin jam'iyyar na Osun ranar Alhamis
- Oyedokun, tsohon mataimakin shugaban PDP na ƙasa ya ce ya ɗauki wannan matakin ne saboda an sauka daga aƙidar da aka kafa jam'iyyar tun usuli
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya samu tangarɗa yayin da ɗaya daga cikin abokansa na siyasa kuma babban jigon PDP ya sauya sheƙa zuwa APC.
Alhaji Shuaib Oyedokun, tsohon mataimakin shugaban PDP na ƙasa ya fice daga jam'iyyar kuma ya sanar da cewa ya rungumi jam'iyyar APC ranar Alhamis, 16 ga watan Mayu.
Jita-jita ta yawaita yayin da Peter Obi ya gana da tsohon gwamnan jihar Jigawa
Oyedokun ya faɗi dalilin komawa APC
Kamar yadda jaridar Punch ta kawo, Oyedokun ya bayyana cewa ya ɗauki matakin sauya sheka daga PDP zuwa APC ne bayan tattaunawa da magoya bayansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fitaccen ɗan siyasar ya ce zai koma tafiyar APC ne saboda yana ganin a can ne za a martaba gogewarsa a siyasa kuma a yabawa kokarinsa da iya shugabanci.
A wasiƙar murabus ɗinsa mai kwanan watan 16 ga watan Mayu, Oyedokun ya ce gurɓata aƙidun da aka kafa PDP na ɗaya daga cikin abin da ya ja hankalinsa ya bar jam'iyyar.
PDP ta rasa shugabanta zuwa jam'iyyar APC
Ya tura wasiƙar murabus ɗinsa daga PDP zuwa shugaban jam'iyya na ƙasa ta hannun shugabannin jam'iyyar na gunduma, ƙaramar hukuma da kuma jihar Osun, Tribune Nigeria ta tattaro.
"Bayan tuntuɓar ɗumbin magoya bayana, na yanke shawarar ɗaukar matakin sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC, inda nake tunanin za a martaba ni kuma a yaba wa ƙoƙarina."Tsohon minista ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC, SGF Akume ya karɓe shi a Abuja
- Alhaji Shuaib Oyedokun
Jiga-jigan PDP na shirin komawa APC
Wannan sauya sheka ta Oyedokun na zuwa a lokacin da ɗan takarar gwamnan da ya marawa baya a zaɓen fitar da gwanin jam'iyyar PDP a 2022 ke shirin shiga APC.
Jam'iyyar APC ta jihar Osun ta ce Dokta Dotun Babayemi da magoya bayansa za su baro PDP zuwa APC a wani rali da aka shirya ranar Jumu'a, 17 ga watan Mayu.
PDP v LP: Atiku ya gana da Peter Obi
A wani rahoton kuma manyan ƴan takarar shugaban ƙasa a 2023, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP sun gana yayin da ake shirin zaɓen 2027.
Atiku wanda tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne ya ce abin alfahari da girma ne da ya karɓi bakuncin tsohon gwamnan jihar Anambra, Obi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoJ6fpdpaWaso6S1sLqMppitmZmirqy1zWaqoa2Xlq%2Biuoypm6llnpZ6rK3SmmSymV2orrbFwGaYZrKlrK5urc%2BcZg%3D%3D